Saturday, January 9, 2021

BIN IYAYE DA YIMASU DA'A 2

 



       



Ya uwana musulmi : Haqqin iyaye yana dauwama ko da iyayen sun mutu, kamar yadda yake ba ya saraya koda iyayen kafirai ne, wajibi ne da ya yi musu biyayya da abu mai kyau, wanda ba sabon Allah ba. Allah Madaukakin Sarki ya ce :


(وَوَصَّيْنَا الْإِنْسَانَ بِوَالِدَيْهِ حَمَلَتْهُ أُمُّهُ وَهْنًا عَلَى وَهْنٍ وَفِصَالُهُ فِي عَامَيْنِ أَنِ اشْكُرْ لِي وَلِوَالِدَيْكَ إِلَيَّ الْمَصِيرُ14 وَإِنْ جَاهَدَاكَ عَلى أَنْ تُشْرِكَ بِي مَا لَيْسَ لَكَ بِهِ عِلْمٌ فَلَا تُطِعْهُمَا وَصَاحِبْهُمَا فِي الدُّنْيَا مَعْرُوفًا وَاتَّبِعْ سَبِيلَ مَنْ أَنَابَ إِلَيَّ ثُمَّ إِلَيَّ مَرْجِعُكُمْ فَأُنَبِّئُكُمْ بِمَا كُنْتُمْ تَعْمَلُونَ15) [لقمان: ١٤ – ١٥].


Ma’ana : *“Mun yi wa mutum wasiyya da iyayensa, mahaifiyarsa ta dauke shi rauni akan rauni, daukan cikinsa da yaye shi shekaru biyu, ka gode min da iyayenka, gareni makoma take. Idan suka tilastaka a kan ka yi shirka da ni cikin abin da baka ilimi a kai, kada ka bi su, ka zauna da su a duniya da kyakkyawa, ka bi hanyar wanda ya mayar da lamarinsa gareni, gareni makomarku take, sai in baku labarin abin da kuke aikatawa”.* (Luqman : 14).


Sannan an karbo daga Asma’u ‘yar Abubakar – Allah ya qara mata yarda – ta ce, mahaifiyata ta zo wajena ziyara a lokacin tana arniya bata musulunta ba, sai na tambayi Annabi (ﷺ) na ce masa : *“Mahaifiyata ta zo wajena tana son (ganina) ko (ya halatta) in sada zumuncinta?” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Eh, ki sada zumuncinta” (ma’ana ki tarbeta, ki ba ta masauki).* Bukhari ne ya rawaito.


Bin iyaye da kyautata musu yana daga cikin manya – manyan ayyukan da suke kusantar da mutum ga Allah Madaukakin Sarki, kuma dalili ne da yake sa Allah ya yaye wa mutum musiba da bala’i, kamar yadda labarin mutanen nan guda uku da suka shiga kogo dutse ya rufe su take nuna wa, yayin da suka cewa junansu “kowa ya yi kamun qafa a wurin Allah da wani aiki na alheri da ya yi, ko Allah ya fitar da mu daga cikin wannan musiba” nan da nan dayansu ya yi kamun qafa a wurin Allah da barin wani aikin sabo da ya yi, sai dutsen ya dan bude kadan. Na biyun ma ya yi kamun qafa da kiyaye amana da ya yi, sai dutsen ya qara bude wa kadan. Na ukun shi kuma ya yi kamun qafa da bin iyayensa da yake yi, ya ce, *“Ya Allah!, haqiqa ni na kasasance ina tare da iyayena tsofaffi guda biyu, da mata ta da ‘ya ‘yana, ina yi wa iyayena kiwon dabbobi, idan na tafi kiwo na tatso nonon dabbobin nan, ina fara bawa iyayena su sha, sannan in bawa iyalina, sai wata rana na yi nisa wurin kiwo, ban dawo ba sai da yamma, na sami iyayen nan nawa sun yi barci, na tatsi nonon nan kamar yadda na saba, na zo da shi, na tsaya a kansu ina jiran su farka in fara ba su, domin ba na son in tashe su daga barcin da suke yi, kuma ba na son in fara bawa ‘ya ‘yana kafin in ba su. Haka na tsaya ina jiransu’ ‘ya’yana suna ta kuka a kusa da ni, amma ban ba su ba, har sai da asuba ta yi, iyayena suka farka na fara ba su, sannan na bawa ‘ya’yana. Ya Allah idan na yi wannan don neman yardarka ka bude mana qofa, sai Allah ya bude musu qofa har suka riqa ganin sama,suka fito suka ci gaba da tafiya”.*


A wannan hadisi mai girma za mu ga yadda wannan bawan Allah ya yi kamun qafa da bin iyayensa, kuma Allah ya yaye masa halin qunci da yake ciki.



*الله تعالى أعلم*



_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​*_



BIN IYAYE DA YIMASU DA'A 1

 



       



Haqqin iyaye a musulunci, haqqi ne mai girma, saboda haka ma Allah Madaukakin Sarki ya hada shi da haqqinsa a wurare da dama a cikin alqur’ani mai girma, kamar fadin Allah :


(وَاعْبُدُوا اللَّهَ وَلَا تُشْرِكُوا بِهِ شَيْئًا وَبِالْوَالِدَيْنِ إِحْسَانًا وَبِذِي الْقُرْبَى وَالْيَتَامَى وَالْمَسَاكِينِ36) [النساء: ٣٦].


Ma’ana : *(Ku bauta wa Allah kada ku yi shirka da shi da wani abu, sannan ku kyautata wa iyaye da makusanta da marayu da Miskinai)* (Annisa’i: 36).


Da fadinsa :


(وَقَضَى رَبُّكَ أَلَّا تَعْبُدُوا إِلَّا إِيَّاهُ وَبِالْوَالِدَيْنِ إِحْسَانًا23) [الإسراء : ٢٣].


Ma’ana : *(“Ubangijinka ya hukunta kada ku bauta wa kowa sai shi kadai, kuma a kyautata wa iyaye)* (Al- Isra’i : 23).


An karbo daga Abdullahi dan Mas’ud – Allah ya yarda da shi – ya ce, na tambayi Manzon Allah (ﷺ) na ce, *“wane aiki ne Allah ya fi so?” sai ya ce, “Sallah akan lokacinta” sai na ce, “Sannan me?” sai ya ce, “Bin iyaye” sai na ce, “Sannan me?” sai ya ce, “Jihadi a kan tafarkin Allah”.* Bukhari da Muslim ne suka rawaito.


An sake karbo wa daga gare shi – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, *“Yardar Allah tana tare da yardar iyaye, fushin Allah yana tare da fushin iyaye”.* Tirmizi da Ibnu Hibban suka rawaito.


Wadannan ayoyi da hadisai suna tabbatar mana da wajabcin bin iyaye da kyautata musu.



*الله تعالى أعلم*



_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​*_



Sunday, January 3, 2021

ARBA'AUNAN NAWAWI COMPLETE


 HADISI NA FARKO (1)


Ankarbo daga umar bini kaddab (r.a) yace manzo Allaah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya lallai dukkanin ayyuka basa ingantuwa (ma,ana basa samun karɓuwa a gurin Allah sai an Qudurce niyya da nufin aikin yazamana dan Allah kayi ba dan wani ba) sai annabi yacigaba da cewa duk wanda yayi hijiri don Allah da manzonsa to sakamakon hijirarsa taga Allah da Manzonsa haka kuma wanda yayi hijirah dan yasamu duniya (ma,ana ai abinda kecikin duniyar misali: kudi, gida ,mata ,gona , )to in yasamu wannan abun to iya rabonsa kenan idan kuma bai samu ba dama badan Allah yayi ba to bazai samu wata lada ba,wanda yayi hijirah don wata mace dayake so ya aura to inya aureta iya rabonsa kenan idan kuma bai samu to bayada wata lada.

 wannan hadisi malamai sun hadu akansa (ma,ana sun inganta shi).


English translation👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

Hadith 1: Deeds are by intentions

Umar ibn Al-Khattab reported: The Messenger of Allah, peace and blessings be upon

him, said:

Verily, deeds are only with intentions. Verily, every person will have only what

they intended. Whoever emigrated to Allah and His Messenger, then his

emigration is for Allah and His Messenger. Whoever emigrated to get something

in the world or to marry a woman, then his emigration is for whatever he

emigrated for.

Source: Ṣaḥīḥ al-Bukhārī 54, Grade: Muttafaqun Alayhi

Like and subscribe us on youtube ALHAQ TV PLUS

https://www.youtube.com/channel/UC5MbqdLbXosUHKtnkmnUcKQ

BIN IYAYE DA YIMASU DA'A 2

          Ya uwana musulmi : Haqqin iyaye yana dauwama ko da iyayen sun mutu, kamar yadda yake ba ya saraya koda iyayen kafirai ne, wajibi n...