Haqqin iyaye a musulunci, haqqi ne mai girma, saboda haka ma Allah Madaukakin Sarki ya hada shi da haqqinsa a wurare da dama a cikin alqur’ani mai girma, kamar fadin Allah :
(وَاعْبُدُوا اللَّهَ وَلَا تُشْرِكُوا بِهِ شَيْئًا وَبِالْوَالِدَيْنِ إِحْسَانًا وَبِذِي الْقُرْبَى وَالْيَتَامَى وَالْمَسَاكِينِ36) [النساء: ٣٦].
Ma’ana : *(Ku bauta wa Allah kada ku yi shirka da shi da wani abu, sannan ku kyautata wa iyaye da makusanta da marayu da Miskinai)* (Annisa’i: 36).
Da fadinsa :
(وَقَضَى رَبُّكَ أَلَّا تَعْبُدُوا إِلَّا إِيَّاهُ وَبِالْوَالِدَيْنِ إِحْسَانًا23) [الإسراء : ٢٣].
Ma’ana : *(“Ubangijinka ya hukunta kada ku bauta wa kowa sai shi kadai, kuma a kyautata wa iyaye)* (Al- Isra’i : 23).
An karbo daga Abdullahi dan Mas’ud – Allah ya yarda da shi – ya ce, na tambayi Manzon Allah (ﷺ) na ce, *“wane aiki ne Allah ya fi so?” sai ya ce, “Sallah akan lokacinta” sai na ce, “Sannan me?” sai ya ce, “Bin iyaye” sai na ce, “Sannan me?” sai ya ce, “Jihadi a kan tafarkin Allah”.* Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
An sake karbo wa daga gare shi – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, *“Yardar Allah tana tare da yardar iyaye, fushin Allah yana tare da fushin iyaye”.* Tirmizi da Ibnu Hibban suka rawaito.
Wadannan ayoyi da hadisai suna tabbatar mana da wajabcin bin iyaye da kyautata musu.
*الله تعالى أعلم*
_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.*_
No comments:
Post a Comment