Ya uwana musulmi : Haqqin iyaye yana dauwama ko da iyayen sun mutu, kamar yadda yake ba ya saraya koda iyayen kafirai ne, wajibi ne da ya yi musu biyayya da abu mai kyau, wanda ba sabon Allah ba. Allah Madaukakin Sarki ya ce :
(وَوَصَّيْنَا الْإِنْسَانَ بِوَالِدَيْهِ حَمَلَتْهُ أُمُّهُ وَهْنًا عَلَى وَهْنٍ وَفِصَالُهُ فِي عَامَيْنِ أَنِ اشْكُرْ لِي وَلِوَالِدَيْكَ إِلَيَّ الْمَصِيرُ14 وَإِنْ جَاهَدَاكَ عَلى أَنْ تُشْرِكَ بِي مَا لَيْسَ لَكَ بِهِ عِلْمٌ فَلَا تُطِعْهُمَا وَصَاحِبْهُمَا فِي الدُّنْيَا مَعْرُوفًا وَاتَّبِعْ سَبِيلَ مَنْ أَنَابَ إِلَيَّ ثُمَّ إِلَيَّ مَرْجِعُكُمْ فَأُنَبِّئُكُمْ بِمَا كُنْتُمْ تَعْمَلُونَ15) [لقمان: ١٤ – ١٥].
Ma’ana : *“Mun yi wa mutum wasiyya da iyayensa, mahaifiyarsa ta dauke shi rauni akan rauni, daukan cikinsa da yaye shi shekaru biyu, ka gode min da iyayenka, gareni makoma take. Idan suka tilastaka a kan ka yi shirka da ni cikin abin da baka ilimi a kai, kada ka bi su, ka zauna da su a duniya da kyakkyawa, ka bi hanyar wanda ya mayar da lamarinsa gareni, gareni makomarku take, sai in baku labarin abin da kuke aikatawa”.* (Luqman : 14).
Sannan an karbo daga Asma’u ‘yar Abubakar – Allah ya qara mata yarda – ta ce, mahaifiyata ta zo wajena ziyara a lokacin tana arniya bata musulunta ba, sai na tambayi Annabi (ﷺ) na ce masa : *“Mahaifiyata ta zo wajena tana son (ganina) ko (ya halatta) in sada zumuncinta?” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Eh, ki sada zumuncinta” (ma’ana ki tarbeta, ki ba ta masauki).* Bukhari ne ya rawaito.
Bin iyaye da kyautata musu yana daga cikin manya – manyan ayyukan da suke kusantar da mutum ga Allah Madaukakin Sarki, kuma dalili ne da yake sa Allah ya yaye wa mutum musiba da bala’i, kamar yadda labarin mutanen nan guda uku da suka shiga kogo dutse ya rufe su take nuna wa, yayin da suka cewa junansu “kowa ya yi kamun qafa a wurin Allah da wani aiki na alheri da ya yi, ko Allah ya fitar da mu daga cikin wannan musiba” nan da nan dayansu ya yi kamun qafa a wurin Allah da barin wani aikin sabo da ya yi, sai dutsen ya dan bude kadan. Na biyun ma ya yi kamun qafa da kiyaye amana da ya yi, sai dutsen ya qara bude wa kadan. Na ukun shi kuma ya yi kamun qafa da bin iyayensa da yake yi, ya ce, *“Ya Allah!, haqiqa ni na kasasance ina tare da iyayena tsofaffi guda biyu, da mata ta da ‘ya ‘yana, ina yi wa iyayena kiwon dabbobi, idan na tafi kiwo na tatso nonon dabbobin nan, ina fara bawa iyayena su sha, sannan in bawa iyalina, sai wata rana na yi nisa wurin kiwo, ban dawo ba sai da yamma, na sami iyayen nan nawa sun yi barci, na tatsi nonon nan kamar yadda na saba, na zo da shi, na tsaya a kansu ina jiran su farka in fara ba su, domin ba na son in tashe su daga barcin da suke yi, kuma ba na son in fara bawa ‘ya ‘yana kafin in ba su. Haka na tsaya ina jiransu’ ‘ya’yana suna ta kuka a kusa da ni, amma ban ba su ba, har sai da asuba ta yi, iyayena suka farka na fara ba su, sannan na bawa ‘ya’yana. Ya Allah idan na yi wannan don neman yardarka ka bude mana qofa, sai Allah ya bude musu qofa har suka riqa ganin sama,suka fito suka ci gaba da tafiya”.*
A wannan hadisi mai girma za mu ga yadda wannan bawan Allah ya yi kamun qafa da bin iyayensa, kuma Allah ya yaye masa halin qunci da yake ciki.
*الله تعالى أعلم*
_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.*_